Isa ga babban shafi
Najeriya

Hankula sun tashi a Maiduguri sakamakon kashe wani soja da fararen hula suka yi

Hankula sun tashi a Maiduri, babban birnin jihar Borno a Najeriya bayan da wasu mutane suka yi wa wani soja rufdugu, suka kashe shi har lahira, bisa zarginsa da harbe fararen hula 4.

Wani sojan Najeriya yayin sintiri a kusa da kogin Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya
Wani sojan Najeriya yayin sintiri a kusa da kogin Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya AFP
Talla

Majiyoyi sun ce a ranar Asabar da ya wuce ne wani kurtun soja mai suna Mohammed Abdullahi ya harbe wadannan fararen hula, biyo bayan wani sabani da ya shiga ktsakaninsu a bangaren kasuwar da ke kan titin Baga na Birnin Maiduguri.

Daya daga cikin wadanda sojan ya harba ya mutu nan take, yayin da saura ukun suka samu munanan raunuka, kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti.

An yi zargin cewa wa, sojin da ya yi harbin, wato Abdullahi, ya kwankwadi barasa ne, kuma take tasiri a kansa a lokacin da ya aikta aika – aikar.

Wasu mjiyoyin sun ce ganin danyen aikin da sojan ya aikata ne ya sa fararen hula da suka fusata, suka yi mai rufdugu, suka afka shi da duka, inda nan take ya ce ‘ga garinku nan’.

Sojan yana aiki ne a bataliya ta 130, amma aka tura shi bataliya ta 212 saboda yakin da ake da ta’addanci a arewa maso gabashin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.