Somalia
Al-Shebab ta kai hari wani Otel a Mogadishu
Akalla mutane uku suka mutu sakamakon harin da kungiyar Al Shebaab ta kai wani otel dake Mogadishu, bayan ta tada bam a cikin wata motar dake kofar shiga ginin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce sojoji sun yiwa otel din da ake kira Hotel Afrik kawanya da kuma tare duk wani hanyar dake zuwa ginin dake hanyar tashar jiragen saman Mogadishu.
Wani jami’in Yan Sanda Mohammed Adan yace anyi musayar wuta tsakanin Yan bindigar da jami’an tsaro wadanda ke kokarin kubutar da jama’ar dake ginin.
Kungiyar Al-Shebaab ta dauki alhakin kai harin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu