Isa ga babban shafi
Sahel

Mutane miliyan 2 sun rasa muhallai a Sahel

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan alkaluman da ke nuna cewa, mutane kimanin miliyan biyu suka rasa muhallansu sakamakon tashe-tashen hankula a yankin Sahel.

Masana sun ce zaman lafiya mai dorewa ne zai hana mutane kaurace wa gidajensu a Sahel.
Masana sun ce zaman lafiya mai dorewa ne zai hana mutane kaurace wa gidajensu a Sahel. © UNHCR/Aristophane Ngargoune
Talla

A yayin zantawarsa da RFI, mai magana da yawun Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Romain Desclous ya bayyana cewa, karuwar adadin mutanen da ke rasa muhallansu a Sahel na da nasaba da rikicin tsawon shekaru biyu da yankin ke fama da shi.

Jami’in ya kara da cewa, a karo na hudu kenan a jere da adadin ke karuwa saboda hare-haren ta’addancin da ake ci gaba da fuskanta a sassan Sahel, inda a farkon wannan shekara aka samu karin mutane dubu 11 da suka rasa matsuguni sakamakon harin da aka kaddamar a wasu kauyuka na Burkina Faso.

Kazalika an samu irin wannan matsalar a makwabciyar kasar wato Jamhuriiyar Nijar a cikin watan Janairu, inda sama da mutane dubu 10 suka kaurace wa gidajensu a dalilin harin ‘yan ta’adda a wasu garuruwa biyu da ke Tillaberi.

Hare-heren ta’addancin dai sun tsananta, lamarin da ke ci gaba da haddasa fargaba a zukutan talakawan da ke rayuwa a kauyuka daban-daban da ke yankin Sahel.

Yanzu haka dai masharhanta kan lamurran tsaro na cewa, sai an samar da zaman lafiya mai dorewa kafin wadannan mutane su koma gidajensu a Sahel.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.