Toh ganin yadda ba kasafai ake samun yadda ake so ba a kowanne gida, ya sa ake yawan zaman cudanni in cudeka tsakanin mata da miji… misali ta hanyar gudanar da ayyuka hade da kula da gida da yara.Sai dai babban kalubalen da matan aure, ma’aikata ke fuskanta shi ne yadda suke hada taura biyu a baki, kuma su tauna lokaci guda, wato kula da yara da maigida da kuma gudanar da aikin ofishi ba tare da samun cikas ba.Zeynab Ibrahim a cikin shirin rayuwata ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki dangane da zamantakewa.Sai ku biyo mu.
Sauran kashi-kashi
-
Yadda matan Nijar suka dage wajen neman kuɗi
Mata a Jamhuriyar Nijar sun dage sosai wajen neman na kansu a maimakon ci gaba da dogara kan mazajensu, yayin da wasu ƙungiyoyi daban daban suka yunkuro domin tallafa wa matan da abubuwan gudanar da sana'o'insu.31/05/202410:00 -
Ra'ayoyin masu sauraren shirin Rayuwata
Shirin Rayuwata na wannan rana ya mayar da hankali ne kan ra'ayoyin masu sauraren sa daga sassan duniya game da shirye-shiryen da suka gabata a wannan makon.30/05/202410:00 -
Bikin Ranar Matan Jamhuriyar Nijar
Shirin Rayuwata na wannan rana ya tattauna ne kan bikin Ranar Matan Jamhuriyar Nijar da ake gudanarwa a duk ranar 13 ga watan Mayu. Ranar ta samo asali tun shekarar 1991, lokacin da matan Yamai suka gudanar da wata zanga-zanga domin kwato ƴancin mata a siyasa.24/05/202410:00 -
Ra'ayoyin Masu Sauraren Shirin Rayuwata
Shirin Rayuwata na wannan rana ya saurari mabanbantan ra'ayoyin jama'a kan shirye-shiryen da aka gudanar a wannan makon.23/05/202410:00 -
Yadda ake tsangwamar matan da suka yi zaman gida yari a Nijar
Shirin Rayuwata na wannan rana ya yi nazari kan yadda jama'ar ke tsangwamar matan da suka taba yin zaman gidan yari a Jamhuriyar Nijar. Matan sun bayyana irin kalubalen da suke fuskanta, suna masu cewa, akan yi musu zinɗe da nuna kyama, yayin da wasu mazan ke cewa, ba za su yarda su yi hulɗa da ire ire waɗannan matan ba.22/05/202410:00