Isa ga babban shafi
Faransa-G5 Sahel

Shugaban Faransa ya gana da takwaransa na Burkina Faso kan taron G5 Sahel.

Emmanuel Macron ya tatauana ne da shugaban kasar ta Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré a wata liyafar cin abinci a wannan larabar, domin shirya zaman taron kungiyar G5 Sahel da zai gudanar a N'Djamenan kasar Chadi, wanda zai maida hankali wajen kara hada hannu domin yakar ayukan ta’addanci tsakanin kasashen na Sahel, kamar yadda fadar shugabancin kasar ta Faransa ta sanar.

Zaman taron  G5 Sahel a Nouakchott, 30 yuni 2020.
Zaman taron G5 Sahel a Nouakchott, 30 yuni 2020. Ludovic Marin /Pool via REUTERS
Talla

Bayan isar sa Faransa daga Bruxelles, daga Beljiyom M. Kaboré ya kasance na karshe daga cikin shuwagabanin kasashen G5 Sahel 5, da shugaban na Faransa ya gana da su tun farko wannan shekara, da suka hada da na Mauritanie, Niger, Tchad da kuma Mali.

Ana sa ran shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci birnin N'Djamena a ranar litanin mai zuwa, domin diga dan baa inda aka kwana, shekara guda bayan zaman taron da shuwagabanin suka gudanar a Pau (dake kudu maso yammacin Faransa) kan matsalolin tsaro a yankin na Sahel, sakamakon tada zaune tsayeen da kungoyin dake ikrarin jihadi ke yi, domin sake fasalta Rundunar dakarun Faransa Barkhane, da kuma fanni da siyasa wajen warware rikicin yankin.

Faransa dake da dakaru dubu 5 a rundunar ta Barkhane, na bukatar rage yawansu.Tare kuma da son ganin aminanta kasashen turai sun shiga batun da himma su kuma kasashen na Afrika sun shimfida wata sabuwar muhimmiyar siyasa a fagen daga.

Baya da baya bayanan aka kashemata dakaru 5, Faransa na fatan ganin ta samu in gantacen sakamako ta fannin soji, tare kuma da bukatar ganin gwamnatocin kasshen na sahel sun samar da wani sabon salon warware rikicin a siyasance a wannan katafaren yanki na Sahel, musaman na kasar Mali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.