Isa ga babban shafi
Faransa-Sahel

Macron na taro da kasashen Sahel kan ta'addanci

Yau shugabannin Kasashen Kungiyar G5 Sahel da shugaban Faransa ke gudanar da taro a kasar Chadi domin tattauna yakin da suke yi kan ‘yan ta’adda a yankin, yayin da Faransa ke tunanin rage yawan dakarunta.

Shugabannin kasashen yankin Sahel
Shugabannin kasashen yankin Sahel Ludovic Marin /Pool via REUTERS
Talla

Taron wanda ake sa ran ya janyo shugabannin kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Jamhuriyar Nijar, zai samu halartar shugaba Emmanuel Macron ta kafar bidiyo.

Wannan shi ne karo na farko da ake gudanar da taron bayan da Faransa ta kara yawan dakarunta a bara domin kara kaimin yakin da ke gudana, amma duk da haka 'yan ta’adda na ci gaba da mamaye wasu yankuna na Sahel.

Akalla sojojin Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin samar da zaman lafiya 6 aka kashe a Mali a cikin wannan shekara, yayin da Faransa ta yi asarar sojojinta guda 5 a watan Disamban bara.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban sojoji da fararen hula sun mutu a yakin, yayin da mutane sama da miliyan biyu suka tsere daga matsugunansu.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a watan jiya ya bayyana shirin sake fasalin ayyukan sojin kasar, sai dai ba a sa ran ya sanar da rage yawan sojin a wannan taro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.