Shugaba Tshisekedi ya nada sabon Firaministan DR Congo
Shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Felix Tshisekedi ya nada Jean-Michel Sama Lukonde Kyenge a matsayin Firaminista bayan kwahse dogon lokaci ana fama da rikicin siyasa a kasar.
Wallafawa ranar:
Sama Lukonde mai shekaru 43 zai maye gurbin Sylvester Ilunga Ilunkamba wanda aka tilastawa barin mukamin sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Tshisekedi da Joseph Kabila.
Kabila da ya taimakawa Tshisekedi hawa karagar mulki kuma suka kafa gwamnatin hadin kai, yanzu haka basa ga maciji da juna a tsakanin su, yayinda Tshisekedi ke gaba da kakkabe mukarraban Kabila daga cikin gwamnatin.
A ranar 29 ga watan Janairu ne Firaminista Sylvester Ilunga Ilunkamba ya yi murabus bayan kada masa kuri’ar yankan kaunar da yan majalisun kasar suka yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu