An kashe sama da mutane dubu 2 a Congo-MDD
Sama da fararen hula dubu 2 suka rasa rayukansu a larduna uku na Jamhuriyar Demokuradiyar Congo a shekarar 2020 sakamakon hare-haren ‘yan bindiga kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, tana mai nuna damuwa kan yadda matsalar ke dada kamari.
Wallafawa ranar:
Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, wuraren da aka tanadar wa mutanen da suka rasa muhallansu a arewacin Kivu na ci gaba da fuskantar hare-hare yanzu haka.
Sama da 'yan gudun hijira dubu 88 ke rayuwa a sansanoni 22 da Majalisar Dinkin Duniya ta samar musu bayan rasa muhallansu a arewacin Kivu.
Rahotanni sun ce, kungiyoyin 'yan bindigan sun mamaye makarantu da gidajen al'umma, yayin da suke kaddamar da farmaki kan cibiyoyin kula da lafiya.
Sama da mutane miliyan 5 rikici ya raba da gidajensu a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo cikin shekaru biyu da suka gabata, inda kididdiga ta nuna cewa, a arewacin Kivu kawai, mutane miliyan biyu aka kora daga gidajensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu