Isa ga babban shafi
Uganda

Kananan yara sun mutu a lokacin da suke wasa da bam

Kananan yara shida sun rasa rayukansu yayin da biyar suka jikkata sakamakon fashewar wani tsohon bam da suke wasa da shi bayan sun tsince shi a dajin arewa maso yammacin Uganda.

An wurgar da bam din ne  a zamanin rikicin 'yan tawayen LRA a Uganda
An wurgar da bam din ne a zamanin rikicin 'yan tawayen LRA a Uganda pmnewsnigeria
Talla

Jami’an tsaron kasar sun bayyana cewa, nan take yara uku suka mutu, sannan aka garzaya da sauran asibitin Adjumani da ke yankin yammacin Kogin Nilu wanda ya yi fama da rikicin tsawon shekaru.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Josephine Angucia ta ce, yaran sun tsinci bam din ne a lokacin da suka shiga dajin domin wasa.

Binciken farko ya nuna cewa, an wurgar da bam din ne kirar gida a zamanin da Kungiyar Lord Resistance Army ke kan ganiyar kaddamar da hare-haren ta’addanci a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, Kungiyar ta LRA ta kashe mutane sama da dubu 100 tare da sace yara kimanin dubu 60 a rikicin da ya bazu zuwa Sudan da Jamhuriyar Demokuradiyar Cingo da kuma Tsakiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.