IS ta dauki alhakin kisan Sojin Tunisa 4 a harin bom
Kungiyar IS ta dauki alhakin kisan Sojin Tunisia 4 a wani farmakin bom da aka kai kan tawagar Sojin ranar 3 ga watan da muke ciki na Fabarairu.
Wallafawa ranar:
IS cikin bayanan da ta wallafa a jaridarta ta Al-Naba da ke bayyana yadda ta shirya kisan Sojin 4 ta kuma bayyana yadda ta yiwa Sojin na Tunisia kutse ranar 20 ga watan Disamban bara a sansaninsu na yankin Kasserine da ke gab da tsaunin Selloum.
Wani bayani da sashen fikira na Amurka mai sanya idanu kan ayyukan ta’addanci ya fitar yau Juma’a ya ce Sojojin 4 sun rasa rayukansu bayan tashin bamabamai har guda 3 a yankin da ke gab da tsaunin Mgila na kasar.
Tun a ranar 3 ga watan nan ne ma’aikatar tsaron Tunisia ta sanar da kisan Sojin a kokarinsu na laluben maboyar ‘yan ta’addar da suka yi sansanin a tsaunin na Mgila.
Tunisia dai na kallon Mgila da Chaambi da ke gab da iyakar kasar da Algeria a matsayin maboyar mayakan ta’addanci da ke kai farmakin sari-ka-noke a sassan kasar.
A jawabin Firaminista Hichem Mechichi, ya ce kisan Sojin 4 ba zai sanyaya musu gwiwa game da damarar da suka daura ta kakkabe ayyukan ta’addanci a sassan kasar ba.
Tun bayan juyin juya halin 2011 da ya hambarar da gwamnatin Zine El Abidine ben Ali, Tunisa ke ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula ciki har da hare-haren ta’addanci wanda ya hallaka gomman Sojin kasar musamman a yankin Kasserine da ke matsayin maboyar mayakan AQIM reshen Al-Qaeda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu