Isa ga babban shafi
Italiya-Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

Italiya ta ce jakadanta ya mutu sakamakon harin 'yan bindiga a Congo

Ma’aikatar harkokin wajen Italiya ta tabbatar da mutuwar jakadan kasar a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, sakamakon harin ‘yan bindiga.

Luigi di Maio ministan harkokin wajen Italiya.
Luigi di Maio ministan harkokin wajen Italiya. REUTERS/Remo Casilli/File Photo
Talla

Sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Italiya ta fitar yau Litinin ne, ta tabbatar da mutuwar jakadan na ta Luca Attanasio a gabashin Dimokaradiyyar Congo.

Ministan harkokin wajen na Italiya Luigi Maio wanda ya bayyana takaicinsa, ya ce lamarin ya auku ne a lokacin da marigayin ke rakiyar ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Goma da ke gabashin kasar.

Di Maio ya ce, "har yanzu ba’a kai ga tabbatar da yanayin mummunan harin ba, amma za su ci gaba da binciken gano musabbi da wadanda suka yi aika-aikar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar jakadan da kuma dogarinsa, dan sandan kasar.

Tun a shekarar 2017, Attanasio mai shekaru 43 ke wakiltar Italiya a Kinshasa, bayan da ya shiga aikin diflomasiyya a shekarar 2003 kuma ya taba yin aiki a Switzerland da Morocco da kuma Najeriya.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen, jakadan da 'yan sandan na daga cikin ayarin motocin MONUSCO, tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Congo.

Wani jami'in diflomasiyya a Kinshasa ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa Attanasio na cikin ayarin motocin Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) lokacin da aka bude musu wuta a kusa da Goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.