Isa ga babban shafi
Senegal

An kama jagoran 'yan adawar Senegal

Jami’an tsaro a Senegal sun kame jagoran ‘yan adawar kasar Ousmane Sonko a birnin Dakar biyo bayan arrangamar da aka yi tsakanin jami’an tsaron da wasu magoya bayansa.

Jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Soko na mika gaisuwa ga magoya bayansa a kan hanyarsa ta zuwa kotu a Dakar
Jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Soko na mika gaisuwa ga magoya bayansa a kan hanyarsa ta zuwa kotu a Dakar AFP - SEYLLOU
Talla

Sonko mai shekaru 46 na kan hanyar zuwa kotu domin fuskantar tuhumar da ake masa kan laifin fyade ne aka baiwa hammata iska tsakanin wasu daruruwan magoya bayansa da ke masa rakiya da jami’an tsaro, wadanda suka afka wa ta hanyar jifa da duwatsu, abin da ya sa su kuma maida martani da barkonon tsohuwa.

Hatsaniyar ce kuma ta kai ga kame Sonko bisa zargin sa da tada zaune-tsaye yayin da yake kan hanyar zuwa kotu.

A watan Fabairu wata ma’aikaciyar shagon yi wa mutane tausa ta shigar da kara gaban kotu bisa tuhumar jagoran ‘yan adawar na jam’iyyar Pastef da yi mata Fyade, zargin da Sonko ya musanta, tare da bayyana shi a matsayin yunkurin shugaban Senegal Macky Sall na hana shi takara a zaben shugabancin kasar na 2024 da ke tafe.

A shekarar 2019 Sonko ya fafata a zaben shugabancin na Senegal, wanda shugaba Sall ya lashe a karo na 2, yayin da shi kuma jagoran ‘yan adawar ya zo na 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.