Isa ga babban shafi
Chadi - 'Yan adawa

Kebzabo ya sha alwashin hana gudanar da zaben shugabancin Chadi

Madugun ‘yan adawar kasar Chadi, Saleh Kebzabo, ya sanar da aniyyarsa ta hana gudanar da zaben neman shugabancin kasar dake tafe ranar 11 ga watan Afrilu, bayan da ya janye takararsa, a zaben da shugaba Idris Deby Itno dake mulki tun a shekarar 1990 ke neman tazarce.

Jagoran adawar kasar Chadi Saleh Kebzaboh, a ranar 18 ga watan Mayun shekarar  200
Jagoran adawar kasar Chadi Saleh Kebzaboh, a ranar 18 ga watan Mayun shekarar 200 DESIREY MINKOH AFP/Archivos
Talla

Saleh Kebzabo wanda ya bayyana Shirin hana zaben ga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, yace bazai fede biri kan hanyoyin da zai bi wajen cimma buri ba, amma dai ta hanyar lumana ce.

"Ba na son in bayyana yadda za mu hana gudanar da wannan zaben shugaban kasa, amma a matsayinmu na 'yan Demokradiya, ba za mu shiga tashin hankali ba," sai dai, dai ku tabbatar da cewa wannan zaben ba zai gudana ba".

"Ba za mu dauki wani mataki na tashin hankali don dakatar da gudanar da wannan zaben ba," in ji Mista Kebzabo, wanda a ranar 1 ga Maris ya janye takarar shugabancin kasar.

Mista Kebzabo wanda sau hudu yake takara da shugaba Deby, ba tare da nasara ba, ya janye takararsa kwana daya bayan wani yunkurin kama wani dan takarar Yaya Dillou Djerou, a gidansa da ke N'Djamena, wanda ya kai ga tashin hankali da aka rasa raykukan akalla mutane uku.

Baya ga Mista Kebzabo, wasu abokan hamayya uku sun janye takararsu, duk da cewa Kotun Koli ta amince da takarsu, suna mai yin allawadai da tabarbarewar yanayin tsaro ga 'yan adawa.

Yanzu haka saura 'yan takara biyar ke shirin fafatawa da Mista Deby wanda ke mulkin Chadi sama da shekaru 30.

Adawa da sake takaran Deby

A ranar 7 ga watan Fabrairu sai da 'Yan sanda a Chadi suka harba barkonon tsohuwa tare da kama mutane da dama a yayin da daruruwan al'umma suka gudanar da zanga – zangar adawa da zaben shugaba Idriss Derby a matsayin wanda zai yi takara a karkashin jam’iyya mai mulki a zaben watan Afrilu mai zuwa don darewa shugabancin kasar a karo na 6.

A babban birnin kasar N’Djamena, daruruwan masu zanga – zanga ne suka kona tayoyi, inda suke ta raira wakokin adawa da wa’adin mulki na shida, suna kuma kira ga Deby ya kama gabansa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Murkushe 'Yan adawa

Majalisar Dinkin Duniya ta kasar Faransa duk sun bukaci gwamnatin Chadi da ta gudanar da bincike kan rikicin da ya barke bayan da jami'an tsaro har da tankokin yaki suka kutsa gidan wani dan adawa Yaya Dillo Djerou, da nufin kama shi, lamarin da yayi sanadiyar rasa rayukan mutane uku, ciki har da mahaifiyar dan adawar, abin da yasa wasu 'yan takara suka janye daga neman shugabancin kasar ciki harda Saleh Kebzabo.

Yayin kare matakin yunkurin kama dan adawar, kakakin gwamnatin kasar ta Chadi Sherif Mahamat Zene, yace jami’an tsaro na gaf da shiga gidan Yaya Dillo ne, wasu mutane da ake kyautata zaton magoya bayan sa ne suka bude musu wuta, abinda ya tilasta musu maida martani domin kare kai, kuma cikin wadanda suka jikkata har da jami’an tsaro uku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.