Isa ga babban shafi

An kaddamar da alluran rigakafin covid 19 a Habasha

Habasha ta soma yiwa mutanen kasar allurar AstraZeneca ta  rigakafin Covid 19 a jiya asabar.Makon da ya gabata ne kasar ta amfana da kusan  allurai milyan 2 da dubu dari 2 daga kamfanin kera maguguna na kasar India kamar dai yada hukumar kiwon lafiya ta Duniya ta tsara a shirin ta na Covax don samarwa kasashe matalauta wadanan allurai cikin sauki kuma a lokaci.

Birnin Addis  Ababa na kasar Habasha
Birnin Addis Ababa na kasar Habasha ©GettyImages
Talla

Habasha dake da yawan al’uma da kusan milyan 110,kasar  na da burin ganin ta yiwa kusan kashi 20 cikin dari wannan alura nan da karshen wannan shekara.Firaministan kasar na ci gaba da kira ga masu hannu da shuni na ganin sun kawo dauki ga kasar ta Habasha,fari,mantsin tattalin arziki,rashin tsaro ,kadan daga cikin matsallolin da kasar ke fama da su yanzu haka.

Hukumomin kasar na ci gaba da fadakar yan kasar don ganin sun yi aiki da matakan karya daga kamuwa da wannan cuta ta Covid 19.

Baya ga kasar ta Habasha,wasu kasashen gabashin Afrika da suka hada da Kenya,Rwanda da Uganda sun kaddamar da yiwa mutan kasar su wannan allura.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.