Zaben yan Majalisu zagaye na biyu a Afrika ta Tsakiya
An soma zaben yan majalisu ,zagaye na biyu a Afrika ta Tsakiya, zaben dake tattare da kalubale sabili da matsallolin tsaro.
Wallafawa ranar:
Akala mutane milyan daya ake sa ran za su fito don kada kuri’un su a dai dai lokacin da majalisar dimkin Duniya ranar juma’a da ta gabata, ta amince da wani shiri na tura karin sojojin ta 3000 da zasu dafawa wajen tabbatar da tsaro a lokacin zaben.
Rahotanni daga bangui babban birnin kasar na nuni cewa gwamnati ta dau matakan tsaro fiye da kima da nufin kare lafiyar jama'a a sassa unguwanin birni ga baki daya.Rasha daga cikin kasashe masu bayar da gundumuwa ta fani tsaro a kasar ,ta bakin mataimakin jakadan kasar a zauren majalisar Dimkin Duniya,ya bukaci Majalisar dimkin Duniya ta kawo karin haske dangane da manufofin da take da su ,har ta dau matakin tura karin sojojin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu