Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

AFCON: Super Eagles ta bi ta ruwa don karawa da Benin a wasan neman gurbi

Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles ta yi amfani da jiragen ruwa wajen shiga Jamhuriyyar Benin don kara wasanta na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta Africa cup of Nation.

Tawagar 'yan wasan Super Eagles gab da tafiyarsu Benin don fafatawa a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika
Tawagar 'yan wasan Super Eagles gab da tafiyarsu Benin don fafatawa a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika © Lagos state government/ Bashir Ibrahim
Talla

Tawagar ta Super Eagle ta zabi bi ta ruwan ne bayanda ‘yan wasanta suka nuna fargabar bin titi saboda lalacewar hanyar da ta sada kasashen na Najeriya da Benin makwabtan juna.

Mai horar da kungiyar kwallon kafar ta Najeriya Gernot Rohr ya ce babu wata fargaba a balaguron tawagar na tsawon sa’a 1 a kan ruwa gabanin isa Benin.

Super Eagles wadda ta kira ‘yan wasanta akalla 20 da ke taka leda a ketare, da safiyar gobe juma’a ne za ta isa Porto-Novo don fara shirye-shiryen karawar.

Super Eagles wadda ta dage kofin har sau 3 a tarihi, ita ke jagorancinta rukuninta na L da maki 8 bayan doka wasanni 4 yayinda Benin ke matsayin ta 2 da maki 7.

Sauran Kasashen da ke cikin rukuni guda da Najeriya sun hada da Sierra Leone mai maki 3 sai Lesotho da maki 2.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.