Idriss Deby ya ziyarci Buhari a Abuja
Shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno ya ziyarci Najeriya inda ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaban Najeriya ba ta yi bayani kan abubuwan da shugabannin suka tattauna a Abuja ba, amma ziyarar Deby na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru ke fuskantar karuwar hare-haren mayakan Boko Haram.
A makwanni biyu da suka gabata, hare-haren ta’addanci sun yi sanadiyar hallaka mutane sama da 200 a Jamhuriyar Nijar.
Shugaba Idris Deby da ya kwashe shekaru sama da 30 a karagar mulki yana takara a zaben da za’ayi ranar 11 ga watan gobe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu