Faransa ta bude Ofishin jakadancinta na Libya bayan shekaru 7
Faransa ta sake bude ofishin jakadancinta da ke birnin Tripoli na kasar Libya, bayan da aka rufe shi shekaru 7 da suka gabata saboda tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan boren da aka yi wa gwamnatin Kanar Kaddafi.
Wallafawa ranar:
Tun cikin makon jiya ne shugaba Emmanuel Macron ya ce za a sake bude ofishin jakadancin, bayan ganawarsa da manzon gwamnatin Libya Mohamed el-Manfi.
Matakin bude Ofishin jakadancin na nuna yiwuwar tabbatuwar zaman lafiya a kasar mai fama da rikici bayan kafa gwamnatin hadin kai gabanin zaben watan Disamba.
Libya ta fada rikici ne tun bayan juyin juya halin 2011 da ya hambarar da gwamnatin kasar tare da hallaka shugaba Muammar Kaddafi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu