Babban Alkali ya tsere daga Benin saboda matsin lambar gwamnati
Wani babban Alkali a Jamhuriyar Benin Essowe Batamoussi ya bayyana tserewa daga kasar saboda abinda ya kira yadda gwamnati ke tirsasa musu wajen gudanar da ayyukan su, musamman shari’un da suka shafi yan adawan dake kalubalantar shugaban kasa Patrice Tallon.
Wallafawa ranar:
Batamoussi yace ya sauka daga mukamin sa a matsayin alkalin dake shari’ar yaki da cin hanci da rashawa da kuma ayyukan ta’addanci wanda ya sanya ido kan tuhumar da ake yiwa Reckya Madogou wadda ta nemi tsayawa takarar zaben shugaban kasa.
Alkalin yace tabbas bashi da ‚yancin gudanar da aikin sa kamar yadda doka ta tanada, kuma akasarin hukunce hukuncen da suka yanke a baya sun yi su ne a karkashin tirsasawa, ciki harda tsare Reckya Madougou.
Hukumomin Benin sun ki cewa komai kan lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu