Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya - Mali

Dakarun MDD sun halaka 'yan ta'adda da dama Mali

Majalisar Dinkin Duniya tace dakarun ta dake aikin samar da zaman lafiya sun kasha mayaka da dama a Mali cikin su harda wani babban kwamandan da ya jagoranci kai hari kan dakarun ta.

Sojojin Mali yayin atsaye a yankin Mopti dake tsakiyar Kamaru.
Sojojin Mali yayin atsaye a yankin Mopti dake tsakiyar Kamaru. AP - Francois Rihouay
Talla

Wata majiya kusa da majalisar tace an kashe kusan mutane 20 daga cikin maharan kusan 100 bayan kwashe sa’oi 3 ana fafatawa lokacin da Yan bindigar suka kai hari sansanin sojin Chadi dake aiki a karkashin Majalisar, abinda yayi sanadiyar kasha 4 daga cikin dakarun.

Kakakin sojin Majalisar Mahamat Saleh Annadif yace sun kidaya gawar Yan bindigar da suka kashe kuma sun zarce 40, cikin su harda Abdallaye Ag Albaka, na hannun daman shugaban Yan Tawaye Iyad Ag Aghaly.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.