Isa ga babban shafi
Kamaru

Sarkin Garoua mai rike da mukamin minista ya rasu

Sarkin Garoua mai daraja ta daya, kuma karamin minista a ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kamaru ya rasu yau, yana da shekaru 75 a duniya.

Marigayi Alim Hayatou, Sarkin Garoua mai daraja ta daya, kuma karamin minista a ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kamaru.
Marigayi Alim Hayatou, Sarkin Garoua mai daraja ta daya, kuma karamin minista a ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kamaru. © Marwainfo
Talla

Gidan radiyo da Talabijin din kasar Kamaru CRTV tace iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a wani asibiti dake jihar ta Arewa wato Garoua, a yau Litinin, bayan watanni yana fama da jinya.

Alim Hayatou wanda ya fito daga babban gida a Garoua dake arewacin Kamaru, wato dangin Hayatou, gidan da Issa Hayatou tsohon shugaban Hukumar Kwallon kafar Afirka CAF da kuma tsohon Firaministan Kamaru Sadou Hayatou suka fito.

Alim Hayatou ya kwashe sama da shekaru 25 ana damawa da shi cikin gwamnatin Paul Biya, kuma ya zama sarkin Garoua a shekarar 2000, bayan rasuwar mahaifinsa Lamido Hayatou.

Marigayi Alim Hayatou, Sarkin Garoua mai daraja ta daya, kuma karamin minista a ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kamaru.
Marigayi Alim Hayatou, Sarkin Garoua mai daraja ta daya, kuma karamin minista a ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Kamaru. © Marwainfo

Marigayin wanda babban Sefeto ne a Baitul-Malin kasa, tun a shekarar 1996 ya zama karamin ministan kiwon lafiyar kasar Kamaru, kuma mai kula da yaki da annoba da cututtuka masu saurin yaduwa.

Rahotanni suka ce, yanzu haka Isah Hayatou na can Garoua ana tsara Shirin jana’ar dan uwansa, wanda ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya 6.

Kawo yanzu ministocin Kamaru biyu ne dake rike da mukamansu suka mutu a cikin wata daya, inda kafin marigayi mai martaba Alim Hayatou, karamin ministan harkokin waje dake kula da kasashen Musulmi da Larabawa Adoum Gargoum annobar korona ta hallaka a farkon watan Maris.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.