Yan Sanda sun harbe mutun daya a garin Butembo
Yan Sanda a garin Butembo na Jamhuriyar Demokkuradiyar Congo sun harbe ha lahira mutun daya a jiya juma’a daga cikin masu zanga don nuna adawar su dangane da rashin tabuka ko wani abin a zo a gani daga rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dimkin Duniya.
Wallafawa ranar:
Yan Sanda a kokarin su na share wasu daga cikin shingaye da masu zanga-zanga suka dasa saman hanyoyi sun fuskanci bore daga masu zanga-zanga,wanda hakan ya kais u ga bude wuta saman su.
Kanal Jean Paul Ngoma shugaban rundunar yan Sanda na garin Butembo ne ya tabbatar da mutuwar mutumen.
Kungiyoyin kare hakokin bil Adam a kasar na ci gaba da kokawa dangane da matakan da yan Sanda ke amfani da su yayin zanga-zangar farraren fula. awasu yankunan kasa ta DRCongo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu