Chadi ta sake fatattakan 'yan tawayen FACT dake neman hambare Deby
Sojojin Chadi sun yi ikirarin “tarwatsa” gungun ‘yan tawaye da suka kai hari arewacin kasar a ranar Lahadi, ranar zaben da shugaban kasa Idriss Déby Itno, da ke kan mulki na tsawon shekaru 30, ke tabbacin nasara.
Wallafawa ranar:
Kakakin rundunar sojin kasar Azem Bermandoa ya sanar da haka maraicen jiya ta karfar talabijin din kasar, yana mai cewa "Jami'an tsaro sunyi nasarar murkushe gungun 'yan tawayen da suka kutsa kai zuwa arewacin Kanem, ba tare da bayyana adadin wadanda aka kashe ba.
A makon da ya gabata, kungiyar ‘yan tawayen FACT wanda ta kunshi sojoji da ‘yan siyasan Chadi galibi kabilan Gorane, wata kabilar Sahara, ta kutsa kai cikin arewacin kasar, tare da ikirarin 'yantar da yankin na Tibesti" a arewacin kasar.
Chadi na fuskantar kutse 'yan tawaye jifa-jifa
Tibesti da kuma garuruwan kan iyaka da kasar Libya, na fuskantar hare-hare daga 'yan tawaye wadanda suke fafatawa da dakarun kasar a kai a kai. A watan Fabrairun shekarar 2019, tawagar ‘yan tawaye da ta taso daga Libya tayi kokarin kifar da gwamnatin Shugaba Idriss Déby Itno, kafin hare-haren Faransa ya tarwatsa su, bisa bukatar N'Djamena.
A watan Fabrairun shekarar 2008, sai da wani harin tawaye ya isa ƙofar fadar shugaban ƙasa kafin a fatattake su tare da goyon bayan Faransa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu