Isa ga babban shafi
Chadi-Deby

Kasashen duniya sun mika ta'aziyar mutuwar Deby

Faransa ta jagoranci kasashen duniya wajen nuna alhinin mutuwar shugaban kasar Chadi Idris Deby wanda ta bayyana shi a matsayin shugaba mara tsoro.

Idriss Déby Itno
Idriss Déby Itno RFI
Talla

A sakon da ta gabatar bayan rasuwar shugaba Deby, fadar shugaban Faransa ta ce Chadi ta yi asarar gwarzon soja kuma shugaban kasa wanda ya yi aiki tukuru wajen samar wa kasar tsaro da zaman lafiyar yankin baki daya na shekaru 30, yayin da ta bayyana shi a matsayin babban abokin tafiya.

Ita kuwa Amurka ta aike da sakon ta’azziya ne ga al’ummar Chadi, inda ta yi Allah-wadai da tashe tashen hankulan da aka samu a kasar wadanda suka kai ga rasa rayuka, yayin da ta bukaci amfani da kundin tsarin mulki wajen daidata siyasar kasar.

Shugaban gudanarwar Kungiyar Kasashen Afirka Moussa Faki Mahamat ya bayyana kaduwar sa da mutuwar Deby wanda ya bayyana a matsayin gwarzo.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa da mutuwar Deby wanda ya ce, ya taka gagarumar rawa wajen yaki da mayakan Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.

Shi ma shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya jajanta wa mutanen Chadi kan rashin da suka yi, mussaman rawar da Deby ya taka wajen jagorancin yaki da yan ta’adda, yayin da ya jaddada aniyarsu ta aiki da kasar wajen tabbatar da zaman lafiya a kungiyar G5 Sahel da kuma Tafkin Chadi.

Shi ma shugaban rikon kwaryar Mali da Firaministan Israila Benjamin Netanyahu duk sun aike da sakon ta’azziyarsu ga mutanen Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.