Isa ga babban shafi
Chadi-Idriss Deby

Tarihin marigayi Idriss Deby Itno

Marshal Idriss Deby Itno mai shekaru 68, na gab da fara wa’adinsa na shida a kan karagar mulki kafin kwatsam mutuwa ta cimma masa a wannan Talata.

Marigayi Idriss Deby Itno na Chadi
Marigayi Idriss Deby Itno na Chadi AP - Ludovic Marin
Talla

Margayi Deby Itno dan makiyaya ne kuma ya shafe shekaru 30 cif yana mulkin kasar, kafin a sanar da mutuwarsa bayan wani gumurzu da ‘yan tawaye a karshen makon da ya gabata.

Mutuwar tasa na zuwa ne kwana guda bayan da rundunar sojan kasar ta sanar da kashe ‘yan tawaye sama da 300, ita kuma ta rasa soja 5.

Idriss Deby ya kasance a sahun gaba wajen kokarin kakkabe masu jihadi da karfin tsiya a kasashen yankin yammacin Afrika.

Shi dai daga kabilar Zaghawa ya fito kuma da aikin sojan ne  ya kai ga mulkin kasar.

A watan Augusta  na shekarar da ta gabata, majalisar dokokin kasar ta girmama shi da mukamin  Marshal, mukami irinsa na farko a kasar Chadi, bayan da ya jagoranci wani gumurzu da masu jihadi da karfin tsiya da suka kashe dakarun kasar akalla 100.

Shugaban Chadi Idriss Deby Itno sanye da kakin soji a fagen-daga da Boko Haram
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno sanye da kakin soji a fagen-daga da Boko Haram wotzup.ng

Yana matashinsa ne, Idriss Deby ya shiga makarantar horas da soja da ke birnin N’Djamena kafin ya wuce kasar Faransa inda ya samu horo a tukin jirgin sama.

Bayan dawowarsa a shekara ta 1979 daga Faransa, ya samu shiga cikin gwamnatin Hissene Habre har aka ba shi hafsan soja bayan da Habre ya kawar da gwamnatin Goukouni Weddeye a shekara ta 1982.

Bayan shekara daya, Idriss Deby ya nuna jarumtaka a yakin da suka yi da ‘yan tawaye da ke samun goyon bayan Libya.

A shekara ta 1989, marigayin ya samu sabani da shugaban kasar bisa zargin take-taken juyin mulki.

Daga nan Idriss Deby ya tsere zuwa Sudan, inda ya yi kokarin hada kan ‘yan tawayan kungiyar Patriotic Salvation Movement wadda ta yi kukan-kura ta shiga N’DJamena  har ta kwace iko a shekara ta 1990.

A shekara ta 1996, shekaru 6 bayan da ya kwace mulki, an zabi Deby a matsayin shugaban kasar a zaben jam'iyyun siyasa irinsa na farko a wannan kasar mai yawan mutane miliyan 11.

Bayan wannan kuma, marigayin ya yi ta lashe zabukan da aka yi ta gudanarwa a kasar, yayin da 'yan adawa ke yi masa kallon mai mulkin kama-karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.