Zazzabin cizon saura ya hallaka mutane a kasar Kamaru
Rahoton masana kiwon lafiya a kasar Kamaru ya nuna cewa kimanin mutane dubu 4121 cutar Zazzabin cizon sauro ya kasha cikin shekara daya a kasar, akasari yara ‘yan kasa da shekaru 5.
Wallafawa ranar:
Rahotan shekara-shekara karkashin wani shirin ma’aikatar lafiyar kasar na yaki da zazzabin cizon sauro, yace adadin masu kamuwa da cutar da kuma mutuwa ya karu asibitocin kasar da akalla dubu 5 a shekarar 2020, idan aka kwanta da shekarar 2019.
Dr. Achu Dorothy dake shugabantar cibiyar ta yaki da cutar zazzabin cizon sauro a kasar ta Kamaru wanda ta jagoranci binciken, tace lamarin yafi kamari a jihohin arewacin kasar uku, wato Maroua da Garoua da kuma Ngaundere.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu