Isa ga babban shafi
Chadi

Gwamnatin sojin Chadi ta ce ba za ta tattauna da 'yan tawaye ba

Sabuwar Gwamnatin mulkin sojin Chadi tace ba zata tattauna da Yan Tawayen da suka kaddamar da hare hare a yankin arewacin kasar ba makwannin da suka gabata da ake zargin su da kashe shugaban kasa Idris Deby Itno.

Mahamat Idriss Deby Itno, sabon shugaban mulkin sojin Chadi.
Mahamat Idriss Deby Itno, sabon shugaban mulkin sojin Chadi. © Tele Tchad via AP
Talla

Wata sanarwar da aka raba wa manema labarai, ta bayyana Kakakin gwamnatin sojin kasar Azem Bermandoa Agouna na cewa wannan ba lokaci ne na tattaunawa ba, kuma babu tattaunawar da za su yi da marasa bin doka.

Tun da farko, kakakin 'yan Tawayen Mahamat Mehdi Ali ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar a shirye suke su tattauna da gwamnati domin ganin an samo maslaha kan halin da kasar take ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.