Isa ga babban shafi
Somalia-Rikici

Fararen hula na tserewa daga Mogadishu saboda rikici

Rahotanni daga birnin Mogadishu na Somalia na cewa dubban mutane na ci gaba da tserewa daga birnin sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnati da kuma ‘yan tawaye.

Wani bangare a birnin Mogadishu na Somalia
Wani bangare a birnin Mogadishu na Somalia Photo : UA-ONU/Stuart Price
Talla

Birnin Mogadishu na fuskantar tarzoma mai muni bayan jinkirin zabe da aka samu, yayin da shugaban kasar ya kara tsawaita wa'adinsa bisa madafun iko, duk da cewa an yi gargadin abin da ka iya biyo baya.

Watanni ana ta tattaunawa karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya ba tare da cimma nasara ba, abin da ya ta'azzara rikicin tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan tawaye.

Babban sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteresh ya bukaci bangarorin biyu da su kiyaye zaman lafiya, yayin da kasar Amurka wadda ke kawance da gwamnatin Somalian, ke gargadin cewa, za ta  lafta wa kasar takunkumin karayar tattalin arzikinta, muddin ba a koma kujerar sulhu ba.

‘Yan sandan Somalia sun sanar a ranar Litinin, an kashe jami'ansu 2 da kuma wani soja guda a fadan da ake yi da 'yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.