Isa ga babban shafi
Sahel-Ta'addanci

Mutane miliyan 29 na bukatar agaji a Sahel-MDD

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji sun bayyana cewar akalla mutane miliyan 29 ke bukatar agajin gaggawa a yankin Sahel sakamakon tabarbarewar tsaro da kuma yunwar da suka addabi kasashe guda 6.

Rikici ya jefa kananan yara cikin bala'in yunwa a kasashen yankin Sahel
Rikici ya jefa kananan yara cikin bala'in yunwa a kasashen yankin Sahel © MICHELE CATTANI/AFP
Talla

Sanarwar hadin gwuiwa da bangarorin biyu suka gabatar sun bayyana kasashen Burkina Faso da Arewacin Kamaru da Chadi da Mali da Nijar da kuma arewa maso gabashin Najeriya a matsayin yankin da aka samu karuwar mutane miliyan 5 da ke bukatar taimako fiye da adadin bara.

Sanarwar ta ce akasarin yankunan da ke wadannan kasashe sun fada cikin tashin hankali na shekaru da dama kamar yadda masu fafutukar kafa kasar Musulunci a arewacin Mali da kuma na mayakan Bugaje 'yan aware. Sai kuma Chadi da arewacin Kamaru da Najeriya da ke fama da nasu tashin hankalin.

Kungiyar agaji ta ‘Norwegian Refugee Council’ da ‘Plan International’ da suka sanya hannu kan takardar sanarwar tare da Majalisar Dinkin Duniya sun ce, sakamakon wannan mummunan yanayi, an rufe dubban makarantu kuma yara sama da miliyan guda da rabi za su fuskanci rashin abinci mai gina jiki.

Chris Nikoi, daraktan shiya na Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce, sun samu karuwar masu fama da yunwa a yankin Afirka ta Yamma da yawansu ya kai kashi daya bisa uku, inda ya kara da cewar, tashe-tashen hankulan sun kuma taimaka wajen kara farashin abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.