Isa ga babban shafi
Somalia

Shugaban Somalia ya amince a yi zabe bayan tashin hankali

Shugaban Somalia Muhammad Abdullahi Muhammad ya bukaci gudanar da zabe da kuma tattaunawa bayan yunkurin tsawaita mulkinsa na shekaru 2 ya gamu da adawa da kuma tashin hankali.

Shugaban Somalia, Muhammad Abdullahi Farmajo
Shugaban Somalia, Muhammad Abdullahi Farmajo © AFP - Mustafa Haji Abdinur
Talla

Yayin gabatar da jawabi ga al’ummar kasar a daidai lokacin da ake ci gaba da takun-saka tsakanin jami’an tsaron gwamnati da na 'yan adawa, shugaban kasa Muhammad ya ce a shirye yake ya shirya zabe cikin kwanciyar hankali, kuma a ranar Asabar mai zuwa zai gurfana a Majalisar Dokoki domin gabatar da shirin zaben.

Shugaban ya bukaci bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar kasar ta ranar 17 ga watan Satumba da su gabatar da kansu domin tattaunawar gaggawa wajen aiwatar da kudirorin da suka amince.

Ita dai wancan yarjejeniya ta bada damar zabin wakilai na musamman wadanda za su zabi 'yan majalisa, su kuma su je su zabi wanda zai zama shugaban kasa a kasar da ke fama da tashin hankali.

Yunkurin tsawaita mulkin shekaru 2 da shugaban ya yi ya gamu da mummunar suka daga kasashen duniya wadanda suka yi barazanar sanya wa kasar takunkumi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.