Isa ga babban shafi
Burkina Faso - Ta'addanci

Ta'addanci ya tagayyara mutane fiye da dubu 17 a Burkina Faso

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya UNHCR ta ce mutane fiye da dubu 17 da 500 ne suka rasa muhallansu a Burkina Faso cikin kwanaki 10 da suka gabata, sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda da suka kashe akalla mutane 45 a baya bayan nan.

Wasu 'yan kasar Burkina Faso da hare-haren ta'addanci ya raba da muhallansu.
Wasu 'yan kasar Burkina Faso da hare-haren ta'addanci ya raba da muhallansu. © UNHCR/Romain Desclous
Talla

Rahoton hukumar kula da ‘yan gudun hijirar na zuwa ne a yayin da ake cigaba da fuskantar karuwar hare-haren gungun ‘yan ta’adda masu biyayya ga kungiyoyin Al Qa’eda da IS tun daga farkon wannan shekara a yankin Sahel, musamman a kasashen Nijar, Burkina Faso da kuma Mali, inda fararen hula suka fi tagayyara.

Hukumar UNHCR ta kuma yi gargadin cewa yanzu haka, matsalar tsaron da ta dabaibaye yankin Sahel ta haifar da gagarumin kalubalen tagayyarar fararen hula cikin yanayi mafi sauri a fadin duniya.

Ko a ranar Litinin da ta gabata, sai da ‘yan bindiga suka kashe kimanin mutane 30 yayin farmakin da suka kai kan wani kauye a gabashin kasar Burkina Faso, kamar yadda majiyoyin tsaron kasar suka tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.