Isa ga babban shafi
Chadi-Zanga-Zanga

Masu zanga-zanga 20 ne suka shiga komar 'yan sandan Chadi

‘Yan sanda a Chadi sun  harbe wani mai zanga zanga tare da kame wasu 20 da suka bijire wa dokar haramta gangami da gwamnatin mulkin sojin kasar da ta karbi mulki bayan mutuwar Marshall Idriss Deby ta saka.

Masu zanga zangar sun kona tayoyi a N'Djamena.
Masu zanga zangar sun kona tayoyi a N'Djamena. AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

‘Yan daruruwan mutane ne suka fantsama titunan babban birnin kasar N’Djamena don gudanar da zanga-zanga  bayan da a yammacin Juma’a gwamnatin sojin kasar ta haramta hakan.

Mai gabatar da kara a babban birnin Youssouf Tom ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa an ji wa mutum daya rauni da harsashi na kwarai, kana 20 suka shiga komar ‘yan sanda.

’Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa gungun masu zanga- zangar a kudancin baban birnin kasar N’Djamena.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.