Gwamnatin Saliyo za ta soke dokar hukuncin kisa a kasar
Mataimakin ministan Shari’ar Saliyo Umaru Napoleon Koroma, ya ce gwamnatin kasar za ta soke zartas da hukuncin kisa nan ba da jimawa ba.
Wallafawa ranar:
Ministan ya bayyana matsayar gwamnatin ta Saliyo ne a ranar Laraba, inda ya ce za su mika kudurin gaban majalisar kasar domin tabbatar da sabuwar dokar ta soke zartas da hukuncin kisa kan masu laifi.
Rabon da a zartaswa da wani hukuncin kisa a Saliyo dai tun shekarar 1998, la’akari da cewar ko da kotu ta yanke hukuncin na kisa ana sassauta ta shi ne.
Kawo yanzu dai ba a fayyace ranar da majalisar kasar ta Saliyo za ta yi muhawara kan kudirin sabuwar dokar shugaba Julius Maada Bio ba, wanda ya ce ya dauki matakin ne domin karfafa ‘yan ci tare da kare hakkokin al’ummar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu