Isa ga babban shafi
Mali-Sojoji

Sojojin Mali sun tsare shugaban kasar da Firaministansa

Tababa da rashin tabbas sun mamaye halin da ake ciki a kasar Mali sakamakon rahotan tasa keyar shugaban kasar, Bah Ndaw da Firaministansa zuwa barikin sojin da ke Kati.

Wasu daga cikin sojojin Mali
Wasu daga cikin sojojin Mali Reuters
Talla

Rahotanni sun ce, matakin ya biyo bayan sauke wasu sojoji guda biyu da ke rike da mukamin ministoci a garambawul din da Firaminista Moctar Ouane ya gabatar a yau Litinin.

Kafin daukar wannan mataki, Firaministan ya ce sojojin kasar da karfi suka tasa keyarsa zuwa ofishin shugaban kasa bayan ya sanar da sabuwar majalisar ministocin wanda bai musu dadi ba.

Ouane ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewar, sauke sojojin guda biyu daga majalisar ministocin ta harzuka sojojin saboda rawar da suka taka wajen gudanar da juyin mulkin da ya kawar da tsohuwar gwamnati.

Wadanda aka sauke daga mukamansu sun hada da ministan tsaro, Sadio Camara da ministan cikin gida Kanar Modibo Kone, inda aka maye gurbinsu da Birgediya Janar Souleymane Doucoure da Manjo Janar Mamadou Lamine Ballo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.