Isa ga babban shafi
Chad-Afrika ta Tsakiya

Chadi na takun-saka da Afrika ta Tsakiya kan kisan sojinta

Kasar Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na takun saka a tsakaninsu bayan da Chadin ta zargi makociyarta da kashe mata sojoji guda 6 akan iyaka, abin da ta bayyana shi a matsayin laifuffukan yakin da ba za ta yafe ba.

Wasu daga cikin sojojin Chad
Wasu daga cikin sojojin Chad AFP - RENAUD MASBEYE BOYBEYE
Talla

Ministan Harkokin Wajen Chadi Cherif Mahamat Zene ya zargi sojojin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kai hari kan sojojinsu da gangan a Sourou.

Gwamnatin Chadin ta ce, an kama sojojin ne guda 5 kafin daga bisani aka harbe su har lahira, yayin da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke cewa musayar wuta aka yi a tsakanin bangarorin biyu.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta bayyana takaicinta da kisan wanda ta danganta  da 'yan tawaye wanda sojojin kasar ke farautar su.

Wannan kisa ya dada tada tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wanda shi ne irinsa na farko tun bayan mutuwar shugaba Idris Deby.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.