Isa ga babban shafi
Sudan

Rikicin Kabilanci ya halaka mutane 36 a Sudan

Wani kazamin tashin hankalin da ya faru a kudancin Darfur Tsakanin Larabawa da wadanda ba Larabawa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 36 a kasar Sudan.

Ana yawan samun rikicin kabilanci a Sudan
Ana yawan samun rikicin kabilanci a Sudan REUTERS/Stringer
Talla

Rahotanni sun ce, fadan ya barke ne a ranar Asabar tsakanin 'yan kabilar Arab al-Taisha da 'yan kabilar Fallata bakaken fata da ke Um Dafuq a Kudancin Darfur.

Kamfanin Dillancin Labaran Sudan ya ce, tuni aka tura tawagar sojoji domin samar da tsaro a yankin bayan mutuwar mutane 36 da kuma jikkata wasu 32.

Eissa Omar mazaunin Um Dafuq ya ce, sun yi ta jin karar manyan makamai lokacin fafatawar da aka yi a karshen mako.

A watan Afrilun da ya gabata, akalla mutane 132 aka kashe a wani rikici na daban a yammacin Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.