Isa ga babban shafi
Mali - Ta'addanci

'Yan ta'adda sun kashe sojojin Mali 6

‘Yan ta’adda sun kashe sojojin Mali 6 a wani farmaki da suka kai musu a yankin tsakiyar kasar, yayin da kuma wasu dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya 15 suka jikkata, sakamakon harin kunar bakin wake da aka kaiwa sansaninsu da mota makare da bama-bamai a kusa da garin Tarkint dake arewacin kasar ta Mali.

Sojojin Mali da na Faransa yayin sintiri a kauyen Bintagoungou, a shekarar 2015.
Sojojin Mali da na Faransa yayin sintiri a kauyen Bintagoungou, a shekarar 2015. AFP
Talla

Dukkanin hare-haren an kai su ne a jiya Juma’a, kamar yadda hukumomin tsaron kasar ta Mali suka tabbatar.

Cikin wata sanarwa, Ministar tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbuer ta ce 12 daga cikin dakarun Majalisar Dinkin Duniyar da suka jikkata sojojinsu ne, guda kuma dan kasar Belgium.

Yanzu haka dai kimanin dakarun majalisar dinkin duniya dubu 13 daga kasashe daban daban ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali, kasar da ta soma fama da masu tayar da kayar baya fiye da shekaru 7 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.