Isa ga babban shafi
AFIRKA-KORONA

Afirka ta Kudu ta tsaurara dokar korona

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sake karfafa dokar takaita zirga zirga na makwanni biyu domin dakile wani sabon nau’in cutar korona wanda ke saurin yaduwa.

Shugaba Cyril Ramaphosa lokacin da yake karbar allurar rigakafi
Shugaba Cyril Ramaphosa lokacin da yake karbar allurar rigakafi GIANLUIGI GUERCIA POOL/AFP
Talla

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar ta kafar talabijin Ramaphosa yace kasar na fuskantar barazanar karuwar cutar a kasar da tafi fuskantar illar annobar a fadin Afirka baki daya.

Shugaban yace yanzu haka asibitocin kasar sun cika sun batse, yayin da gadajen kwanciya a dakunan da ake kula da wadanda rashin lafiyar su ta yi tsanani suka karanta, abinda ya sa ya daga matakin yanayin barazanar da suke fuskanta zuwa mataki na 4.

Ramaphosa ya sanar da haramta taruwan jama’a sabanin masu halartar jana’iza da aka ce ba za su wuce mutane 50, tare da haramta sayar da giya ko kuma barasa a fadin kasar.

Sabbin matakan da shugaban ya sanar sun hada da hana mutane zama su ci abinci a gidajen da ake sayarwa, sai dai su saya su tafi ko kuma su sa a kai musu gida, tare da tsawaita dokar hana fitar dare da awa guda.

Shugaban yace illar sabon nau’in cutar da aka fara ganowa a kasar India na iya zarce wadanda aka gani a cikin kasar yayin da suke kokarin fadada gabatar da allurar rigakafi ga jama’a.

Mutane miliyan guda da dubu 928 da 897 suka harbu da cutar a Afirka ta kudu, yayin da dubu 59,900 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.