Isa ga babban shafi
Mali - Faransa

Faransa za ta ci gaba da ayyukan hadin gwiwa na soja da Mali

Faransa ta sanar da shirin ci gaba da ayyukan hadin gwiwar dake tsakaninta da Mali ta fuskar soji, bayan dakatar da ayyukan da ta yi a farkon watan Yuni, sakamakon juyin mulkin da sojojin kasar suka yi sau 2 cikin watanni 9 a karkashin jagorancin Kanal Assimi Goita.

Sojojin Faransa a garin Gao dake arewacin kasar Mali.
Sojojin Faransa a garin Gao dake arewacin kasar Mali. Philippe Desmazes AFP/Archivos
Talla

Faransa ta ce matakin ya biyo bayan ganawar da tayi da wakilan gwamnatin rikon kwaryar sojin kasar ta Mali da kuma sauran kasashen yammacin Afrika dangane da tabbacin shirya zabe a watan Fabarairun 2022 don sake mikawa farar hula mulki.

A ranar 10 ga watan Yunin da ya gabata shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da kawo karshen ayyukan rundunar Barkhane mai kunshe da dakarun kasar dubu 5 da 100 a Mali, inda ya ce daruruwa daga cikin sojojin na Faransa za su jagoranci ayyukan sabuwar rundunar yaki da ta’addanci a yankin Sahel mai suna Takuba, wadda a yanzu haka ke da dakaru 600 rabinsu kuma Faransawa.

Tuni dai kasashen da suka hada da Jamhuriyar Czech, Estonia, Italiya, Romania da kuma Sweden suka yi alkawarin bada gudunmawar dakarunsu wajen karfafa sabuwar rundunar ta Takuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.