Isa ga babban shafi
AFIRKA-KORONA

Bincike ya nuna karuwar masu harbuwa da cutar korona a Afirka

Wani bincike ya nuna cewar kasashen Afirka sun samu karuwar masu harbuwa da cutar korona a makon jiya wanda yawan su ya kai sama da 36,000 kowacce rana, abinda ya jefa fargaba a tsakanin hukumomin kula da lafiya.

Shugaban kungiyar kasashen Afirka Felix Tshisekedi
Shugaban kungiyar kasashen Afirka Felix Tshisekedi REUTERS - POOL
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace alkaluman da ya tattara ya nuna cewar tsakanin ranar 28 ga watan Yuni zuwa 4 ga watan Yulin wannan shekarar mutane dubu 36,141 suka harbu da cutar sabanin dubu 32,609 aka gani a watan Janairu.

Kasar Afirka ta Kudu ke sahun gaba wajen yawan masu harbuwa da cutar wanda yawan su ya kai dubu 26 a karshen mako sakamakon sabon nau’in cutar da ake kira Delta dake saurin yaduwa da aka samu.

Rahotan yace adadin mutane 8,000 da ake ganin suna kamuwa da cutar a watan Mayu ya tashi saboda samun karuwar kashi 23 na sabbin masu kamuwa da cutar abinda ke tabbatar da samun karuwar masu fama da cutar.

Kasashen Afirka na fama da matsalar yiwa jama'ar kasashen su rigakafi saboda gazawa wajen samun maganin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.