Isa ga babban shafi
Sahel - Yunwa

Mutane fiye da miliyan 17 na fama da yunwa a yankin Sahel – Oxfam

Kungiyar agaji ta Oxfam ta bayyana kasashen Burkina Faso da Chad da Mali da Mauritania da Nijar da Najeriya da kuma Senegal a matsayin masu fama da matsalar yunwar da girmanta ya kai kashi 67 cikin 100.

Wani karamin yaro ta yunwa ta tagayyara a kauyen Beraketa dake yankin Kudancin kasar Madagascar.
Wani karamin yaro ta yunwa ta tagayyara a kauyen Beraketa dake yankin Kudancin kasar Madagascar. AP - Laetitia Bezain
Talla

Rahoton kungiyar ya ce akalla mutane 11 ke fuskantar barazanar mutuwa a cikin ko wane minti guda a fadin duniya sakamakon yunwar da rashin abinci mai gina jiki.

Rahoton da kungiyar Oxfam ta wallafa ya ce mutane kusan miliyan 17 da rabi ne ke fama da matsalar karancin abinci a Yankin Sahel da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda ya nuna karuwa daga adadin sama da miliyan 6 da rabi da ake da shi bara.

Kungiyar ta bayyana tashin hankali a matsayi babban dalilin haddasa matsalar yunwa a kasashen Burkina Faso da arewacin Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wadanda suka fi jin radadin matsalar.

Wata mata rike da jaririnta a sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Barsalogho dake kasar Burkina Faso.
Wata mata rike da jaririnta a sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Barsalogho dake kasar Burkina Faso. © Thomson Reuters Foundation/Nellie Peyton

Oxfam ta ce a Burkina Faso kawai an samu karuwar yunwar da girmanta ya kai sama da kashi 200 tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020, yayin da ake hasashen cewar matsalar na iya kaiwa kashi 317 a bana.

Ku latsa alamar sauti domin sauraren hirar da Bashir Ibrahim Idris ya yi da Assalama Dawalack Sidi, Daraktar kungiyar da ke kula da Yankin Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya

03:41

Hira da Assalama Dawalack Sidi kan matsalar yunwa a Afrika

Rahoton ya ce tashin hankalin da ake samu a Yankin Sahel da Tafkin Chadi ya tilastawa mutane kusan miliyan 5 da rabi barin gidajensu, kuma akasarinsu manoma ne.

Oxfam ta ce a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mutane kusan dubu 340 aka tilastawa barin gidajensu sakamakon tashin hankali a watan Disambar bara, abinda ya hana su zuwa gonakinsu domin yin noma.

Rahoton kungiyar ya ce duk da wadannan matsaloli kasashen Najeriya da Mali da Burkina Faso da Chadi da kuma Nijar sun kara yawan kudin da suke kashewa bangaren aikin soji da ya kai dala miliyan 930 wanda ya kai adadin da ake bukata wajen aikin jinkai a kasashen Burkina Faso da Mali.

Kungiyar ta bayyana cewar lokaci na kurewa wajen ceto rayukan jama’a yayin da ake hasashen samun karuwar mutanen da za su fuskanci matsalar yunwar su zarce miliyan 27 nan da watan Agusta mai zuwa.

Wata Dattijuwa 'yar kasar Somalia bayan shiga sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Doolow, a kudancin kasar Somalia.
Wata Dattijuwa 'yar kasar Somalia bayan shiga sansanin 'yan gudun hijira dake yankin Doolow, a kudancin kasar Somalia. © AFP

Oxfam ta bukaci gwamnatoci da masu bada agaji da su gaggauta taimakawa shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya domin kaiwa wadannan mutane dauki.

Kungiyar ta ce ta taimakawa mutane sama da dubu 700 a Yankin Sahel tun bayan barkewar annobar Korona, yayin da ta hada kai da masu taimaka mata wajen tallafawa mutane sama da dubu 60 a Chadi wajen basu kudade da abinci.

Oxfam ta kuma ce ta tallafawa mutane dubu 280 a Nijar da Senegal domin tunkarar tsadar rayuwa sakamakon annobar Korona ta hanyar basu abinci da ruwan sha da taimakon kudade da kayayyakin kula da lafiya.

Kungiyar ta ce burin ta shine kaiwa ga miliyoyin mutanen dake bukatar taimako a watannin dake tafe, abinda ya sa take neman taimakon kudade daga masu bada agaji na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.