Rwanda - Mozambique
Rwanda zata tura sojoji 1000 don taimakawa Mozambique
Kasar Rwanda ta bayyana shirin tura sojojinta dubu daya zuwa kasar Mozambique, domin taimaka wa kasar yaki da ‘yan ta’adda a lardin Cabo Delgado.
Wallafawa ranar:
Talla
Rwanda ta amince ta tura sojojin ne bayan da taron shugabannin kasashen yankin kudancin Afrika karkashin inuwar kungiyarsu ta SADC ta bukaci a taimaka wa kasar don murkushe ‘yan ta’addan.
Daga shekarar 2017 zuwa farkon wannan shekara, fadan da aka gwabzawa a yankin na Cabo Delgado, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dubu biyu da 900 tare da tilasta wa sama da dubu 800 barin gidajensu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu