Isa ga babban shafi
Morocco-Bakin-haure

Sojojin Morocco sun ceto bakin haure 344 a tsakiyar teku

Jirgin sojin ruwan Morocco ya ceto bakin haure 344, cikinsu har da mata da yara a teku lokacin da kwale-kwalensu marasa inganci suka fuskanci matsalar a tsakiyar tekun meditereniya.

Mutane da dama na hallaka a teku a kokarinsu na zuwa Turai
Mutane da dama na hallaka a teku a kokarinsu na zuwa Turai REUTERS - JON NAZCA
Talla

Majiyar sojin kasar ta ce, akasarin bakin sun fito ne daga yankin Afirka da ke kudu da sahara, kuma an ceto su ne tsakanin ranar Asabar zuwa Larabar wannan mako.

Sanarwar ta ce, an bai wa mutanen agajin gaggawa kafin kai su gabar ruwa mafi kusa, inda aka mika su ga jami’an Jandermerie.

Da dama daga cikin 'yan ci-ranin Afirka na hallaka a teku a yayin yunkurinsu na tsallakawa zuwa kasashen Turai domin samun ingancin rayuwa bayan sun guje wa kasashensu saboda talauci da rikice-rikice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.