Isa ga babban shafi

Masu rajin kare hakkokin Bil Adam a Tunisia na adawa da matakin Shugaban kasar

Kungiyoyin kare hakkokin bil Adam a Tunisia a yau asabar sun bayyana damuwa tareda yin Allah wadai ganin ta yada Shugaban kasar ke ci gaba da nuna karfin iko tareda kama yan siyasa da suka hada da  wani dan Majalisa  da ake kalo a matsayin mai suka ga gwamnati mai ci yanzu haka.

Shugaban kasar tunisia  Kaïs Saïed,
Shugaban kasar tunisia Kaïs Saïed, REUTERS - Zoubeir Souissi
Talla

An dai kama Yassine Ayari ne a jiya juma’a,dan majalisar da a baya ya fuskanci tarin dauri sabili da ra’ayin da yake da shi a kan wannan gwamnati.

Harabar majalisar dokkokin kasar ta Tunisia
Harabar majalisar dokkokin kasar ta Tunisia © AP - Hedi Azouz

Kotun sojin  kasar ta Tunisia ta tabbatar da kama dan Majalisar dake tsare yanzu haka.

Yayinda kasashen Duniya ke ci gaba da kira don ganin an cimma zaman lafiya a wannan kasa,Shugaban kasar ya bayyana fatan sa na ci gaba da yaki da miyagun dabbi'u,banda haka zai mayar da hankali weajen yaki da cutar Covid 19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.