Gwamnatin Algeria na binciken kisan mutumin da ake zargi da tada gobara
Gwamnatin Algeria na binciken musabbabin kashe wani mutun da ake zargi da hannu wajen tashin mahaukaciyar gobarar daji da kasar bata taba ganin irinsa ba.
Wallafawa ranar:
Tun ranar littini data gabata gobarar ke ta barna a Algeria inda mutane akalla 69 suka rasa rayukansu.
Wani hoton Bidiyo da aka watsa a shafukan sada zumunta ranar Laraba nan una yadda mutane aka yi ta dukan mutumin mai shekaru 38 mai suna Jamal Ben Ismaila har lahira.
Mutanen na zargin babu shakka shine musabbabin gobarar dake ta barna a kasar
Babban mai shigar da kara na Gwamnati na cewa za’a yi cikakken binciken wannan kisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu