Isa ga babban shafi
Uganda

Uganda ta dakatar da ayyukan wasu kungiyoyi 54 a kasar

Gwamnatin Uganda ta bada umarnin dakatar da ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu har guda 54 a kasar, abin da ke kara tabbatar da yunkurinta na dakile kungiyoyin fararen hula a kasar.

Yoweri Museveni, président sortant de l'Ouganda, brigue un 6e mandat.
Yoweri Museveni, président sortant de l'Ouganda, brigue un 6e mandat. © RFI
Talla

Daga cikin kungiyoyin da matakin ya shafa har da Chapter Four wadda ta shahara wajen kare hakkin bil’adama a Uganda da kuma kungiyoyin addinai da na kare muhalli da na demokuradiya.

Hukumar da ke sanya ido kan kungiyoyi masu kansu da ke karkashin Ma’aikatar Cikin Gidan kasar ta Uganda, ta ce, wannan umarnin dakatarwar ya fara aiki nan take.

Hukumar ta ce, wadannan kungiyoyi sun gaza mutunta dokar gudanar da ayyukansu ciki kuwa har da kin sabunta takardun izinin wanzuwarsu a kasar.

Kazalika wasu daga cikin kungiyoyin sun ki yin rajista da hukumomin kasar.

Daga cikin kungiyoyin da matakin ya shafa, har da wadanda suka sanya ido a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a watan Janairu, inda a wancan lokacin jami’an tsaro suka kai musu samame tare da cafke shugabanninsu.

Shugaban kasar Yoweri Museveni ya lashe zaben kasar na wancan lokaci bayan gudanar da yakin neman zabe cikin tashin hankali da cin zarafin ‘yan adawa har ma da far wa gidajen jaridu, baya ga kisan gomman mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.