Isa ga babban shafi
Chadi - Sahel

Chadi za ta janye sojojinta 600 daga rundunar G5 Sahel

Gwamnatin Chadi ta sanar da shirin janye sojojinta 600 daga cikin dubu 1 da 200 da ke yaki da ‘yan ta’adda a karkashin rundunar G5 Sahel, inda hare haren yan ta’adda yayi sanadiyar kashe dubban rayuka a kasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.

Sojojin kasar Chadi.
Sojojin kasar Chadi. AFP PHOTO / MIGUEL MEDINA
Talla

Kakakin rundunar sojin Chadi AbdeRahman Koulamallah ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa janye rabin dakarun nasu daga rundunar G5 Sahel dabara ce ta fuskantar sabuwar barazanar ‘yan ta’adda da ke neman kunno kai.

Kan iyakoki uku tsakananin Mali, Burkina Faso da Nijar tare da tsakiyar Mali, ne yankunan da suka fi fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da suka kashe sojoji da fararen da dama a yankin Sahel.

Hari na baya bayan nan na masu ikirarin jihadi suka kai, shi ne na kauyen Thiem da ke yankin Tillaberi a Jamhuriyar Nijar,  inda suka kashe mutane akalla 17 ranarAsabar da ta gabata.

Kasar Chadi dai na fama da ta ta matsalar ta ‘yan ta’addana masu ikirarin Jihadi a yankin Tafkin Chadi da ke iyaka da Nijar da Najeriya da kuma Kamaru.

A farkon watan nan, mayakan da ake kyautata zaton na Boko Haram ne a yankin Tafkin na Chadi suka kashe sojojin kasar 26, tare da raunata wasu 14.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.