Isa ga babban shafi

Dan jarida Amadou Vamoulke ya sake bayyana a gaban kotun Kamaru

Dan Jarida Amadou Vamoulke ya sake bayyana a gaban kotun kasar Kamaru bayan kwashe sama da kwanaki 1,802 ana tsare da shi ba tare da samun sa da laifi, lauyoyin Kamaru da na Faransa sun bayyana damuwa kan ci gaba da tsare shi na kusan shekaru 5 ba tare da bin ka’ida ba.

Amadou Vamoulke gaban alkali
Amadou Vamoulke gaban alkali © Wikipedia
Talla

Yayin zaman na kotu a yau juma’a,masu shigar da kara sun kasa kawo cikakkun wujoji dangane da tuhumar da ake yi masa.

Amadou Vamoulke
Amadou Vamoulke © Wikipedia

Lauyoyin sun ci gaba da bayyana matukar damuwar su kan halin da Vamoulke ke ciki da kuma musamman tabarbarewar lafiyar sa da kuma yunkurin bata masa suna ba tare da gabatar da kwararan shaidu ba dangane da zargin da ake masa a shari’ar da taki ci taki cinyewa.

Amadou Vamoulke 2
Amadou Vamoulke 2 © Wikipedia

A yan watanni da suka gabata dai likitocin Kamaru da na Faransa duk sun tabbatar da rashin lafiyar da Amadou Vamoulke mai shekaru 71 ke fama da shi abinda zai jefa rayuwar sa cikin hadari.

Alkali ya dage shara’ar zuwa ranar 10 ga wannan watan da muke cikin sa .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.