Isa ga babban shafi
Guinea

An jiyo karar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasar Guinea

Rahotanni daga Guinea Conkary sun ce an jiyo karar harbe-harbe a tsakiyar babban birnin kasar da safiyar Lahadi, kuma an ga sojoji a kan tituna, kamar yadda shaidu gani da ido suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wasu sojojin kasar Guinea.
Wasu sojojin kasar Guinea. © Reuters
Talla

Babu dai cikakken bayani game da abubuwan da suka faru a yankin Kaloum da ke Conakry babban birnin Guinea, inda fadar shugaban kasa, cibiyoyi daban-daban da kuma manyan ofisoshi suke.

Har zuwa lokacin wallafa wannan labarai kuma hukumomi a kasar da ke Yammacin Afirka ba su ce komai kan lamarin ba.

Sai dai wasu ‘yan kasar da aka tuntuba ta wayar tarho a Kaloum sun tabbatar da rahoton jin karar harbe-harben, zalika akwai sojoji da dama a kan tituna wadanda suka yi kira ga mazauna garin da su koma gidajensu su ci gaba da zama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.