Isa ga babban shafi
Mali

MDD ta gargadi sojojin hayan Rasha dake shirin zuwa Mali kan hakkin dan adam

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi sojojin haya da ke Shirin aiki da gwamnatin Mali kan "mutunta haƙƙin ɗan adam da dokokin ƙasa da ƙasa.

Shugaban rikon kwarya Mali Kanal Assimi Goïta, Yayin wani taron soji a Bamako 7/6/21.
Shugaban rikon kwarya Mali Kanal Assimi Goïta, Yayin wani taron soji a Bamako 7/6/21. AFP - ANNIE RISEMBERG
Talla

Da aka tambaye shi a wani taron manema labarai game da yuwuwar tasirin tura sojojin hayar na wani kamfanin tsaro na kasar Rasha Wagner  kimanin 15 don aikin wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya kan Ayyukan Zaman Lafiya, ya ce, dole a mutunta dokokin kasa-da-kasa.

Faransa da Jamus sun yi gargadin cewa za su sake duba ayyukansu na soji a kasar Mali muddun shugabannin sojin kasar suka kulla kawance shigo da sojojin haya daga kamfanin Wagner na kasar Rasha da ake takaddama akai, wanda tuni ya kasance a wasu kasashen Afirka da dama.

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Majalisar Dinkin Duniya ta zargi membobin wannan kamfanin aikin samar da tsaro, wanda ake ganin na kusa-kusa ne ga Shugaba Vladimir Putin, da aikata cin zarafi a farkon wannan bazara duk da cewa adadin wadancan zarge -zargen ya ragu, in ji wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.